Muna Murna Da Ziyarar Da Aka Kawo Mana

Muna Godiya Da Farin Ciki Ga Duk Gudun Mawar Shawara Dag Zaku Iya Bamu,

Sai Munji Daga Gare ku.

Friday, June 5, 2015

ASSUNANUL FI’ILIYYA

Sunnonin da aka aikata su da gabbai

1) ITTIKHA’ZUL SITRU FISSALATI (SANYA SUTRA ACIKIN YIN SALLAH) 
Sunna ne akkan massala’ta su sanya sutra a gabansa dan kare abin da ze gifta a gabansa dan cewarsa annabi (SAW) idan dayanku zai yi sallah ya sanya sutra ya kusance ta shaitani ba zai yanke mar sallah ba. Rawi (Abu Dawud 681)

TANBIHI (TUNATARWA)
Wannan sutra da muka ambata ko wani bango ko abin dogara ko wata sanda da za a iya kafa koma me ma za a iya sitra da su. Ko misali karshen sirdi na abin hawa Da kuma cewarsa annabi (SAW) idan dayanku ya sanya a gabansa sitra kamar misali karshen sirdi na abun hawa babu damuwa kan mai wucewa ta gabansa Rawi (Muslim 499, Tirmizi 33)

 2) Raf’ul yadaini inda takbiratul ihram wa indarruku’i warraf’u minhu wa indal qiyami minattashahuddil auwal wa kazalika inda kulli raf’in wa qafdin (daga hannaye guda biyu a yin kabara harama da lokaci yin ruku’u da dagowa daga ruku’u da tashi bayan gama tahiyar farko haka a dukkan dagowa da tafiya) An samo hadisin daga Nafi’i yace Abdullahi dan Umar ya kasance idan zai shiga cikin sallah yana yin kabbara yana daga hannayensa idan zai yi ruku’u ma yana daga hannayensa, idan yace samiallahu liman hamidahu yana daga hannayensa sannan idan ya dago daga raka’a ta biyu yana daga hannayensa. Abdullahi dan Umar ya mika wannan Magana cewa daga wajen annabi ya’ga yanayin haka. Rawi (Bukhari 739, Muslim 504)  

TANBIHI (TUNATARWA)
Wadannan gurare guda hudu da muka ambata cikin wannan hadisin su ne inda karfafa daga hannaye sai dai sunnah ne wani lokaci (ahyanan) daga hannaye a ko wace dagowa ko tafiya saboda hadisin da aka samu daga Maliku ibnul Huwairis lallai shi ya ga annabi da idonsa yana daga hannayensa idan zai yi ruku’u kuma yana daga hannayensa idan zai dago daga ruku’u idan zai tafi sujjada haka idan zai dago daga sujjada, yana daga hannayensa kusa da kunnuwansa. Rawi (Nasa’i vol. 2 hadiths 206)

MUHALLURRAF’I WA SIFFATIHI (WAJAJEN DAGA HANNU DA YADDA AKE YI)

a. Ya tabbata daga annabi (SAW) ya kasance yana daga hannayensa wani lokaci taren da yin kabbara. b. Wani lokacin kuma bayan yin kabbara
c. Wani lokacin kuma kafin yin kabbara

3) WAD’UL YUMNA ALAL YUSRA FAUKASSADRI (DAURAN HANNUN DAMA AKAN HANNUN HAGU AKAN KIRJI)

a) An samo hadisin daga Sahal bin Sa’ad ya ce mutane sun kasance ana ba’su umarni akan su daura hannayensu na dama akan zira’i hannun hagu acikin sallah. Rawi (Bukhari 740, Malik Muatta 376). 

b) An samo hadisin daga Wa’il bin Hujirin yace na yi sallah tare da annabi (SAW) sai ya daura hannunsa na dama akan na hagu akan kirjinsa acikin sallah. Rawi (ibn khuzaima 479) Albani ya inganta wannan hadisin a littafinsa irwa’ul ghalil 352

4) ANNAZRU MUHALLISSUJUD (KALLON GURIN SA GOSHI) Aisha uwar muminai ta ce yayin da Annabi (SAW) shiga ka’aba idonsa bai saba wa kallon gurin sujjadassa ba ma’ana idonsa yana kallon inda goshinsa yake tabawa Rawi (Alhakim 479)

5) ISTIWA’UZZAHR FIRRUKU’U WA ADAMU RAF’URRASI AU KHAFDUHU WAL QABDU BIL KAFFI ALARRUKUBATAINI MA’ATAFRIJUL ASABI’I WAMUBAADATUL ADUDAINI ANIL JAMBAINI (DAIDAITA GADON BAYA ACIKIN RUKU’U KADA A DAGA KAI SAMA KAR A KWANTAR DA SHI CHAN KASA DA BUDA TAFIKAN HANNU A DANKI GUIWA DA SU DA NISANTAR DA MANNE HANNAYE GUDA BIYU ACIKIN JIKI).

a. Saboda hadisin Abi Humaid acikin irin siffar sallah annabi (SAW) idan ya yi ruku’u yana daura hannayensa akan guiwowinsa sannan ya mike gadon bayansa har sai ya zama ya daidaita shi bai karkata ba. Rawi (Bukhari 821, Abu Dawud 717). b. Hadisin uwar muminai ta ce annabi (SAW) ya kasance in ya yi ruku’u baya daga kansa sama sai dai yana daidaitawa sakani. Rawi (Muslim 498, Abu Dawud 768)

SUNNONIN SALLAH

Sun kaso kashi biyu
1.  Sunnonin da za a firta da baki (kauliyya)
2.  Sunnonin da za a aikata da gabbai (fi’íliyya)
Sunnonin da za a firta da ba’ki sun kaso kashi goma
 • Karatun surah bayan fatiha
Sunnah ne karanta surah a rakaóin farko bayan fatiha da ijma’in mallamai (taruwan mallamai) haka kuma sunnah ne karanta surah a raka’oin karshe (raka’ah uku da ta hudu)

DALILI (HUJJA)
Hadisin Abi qata’dah yace manzan Allah (SAW) ya kasance yana karanta a raka’oin farko fatiha da surah yana jiyar da mu ayah wani lokacin yana karantawa a raka’oin biyun karshe da suratul fatiha.
Rawi (muslim 421, bukhari 759).

Amma karantun surah a raka’a  uku da ta hudu an samu ne a hadisin Abi sa’idin lallai  manzan Allah (SAW) ya kasance yana karanta a raka’oin biyun farko na azahar ayoyi talatin talatin sannan a biyun karshe da ayoyi goma sha biyar biyar.
Rawi (muslim 452)
 • Zikiri cikin ruku’u
Allahumma laka raka’atu wa laka aslamtu wa bika a’mantu qhasha’a laka sam’i wa basari wa mukki wa azmi wa asabi
Rawi (muslim 771, tirmizi 4371, Abu dawud 760)
·        Subhanaka Allahumma rabbana wa bi hamdika Allahumma  agfirli
Rawi (bukhari 247, muslim 484)
·        Subbuhun quddusun rabul mala’ikati wa ruhh
Rawi (muslim 487)
·        Subhana zil jabaruti wal malakuti wal kibriya’u wal azma
Rawi (Abu dawud 873)
 • Azikru baádal kiyam minal ruku’i wa ba’ada rabbana walakalhamdu (zikir bayan dagowa daga ruku’u da kuma bayan rabbana walakalhamdu)
Allahumma rabbana walakalhamdu mil’assamawati wa mil’al ardi wa mil’a ma bainahuma wa mil’a ma shita min shay’in baada ahlusana’i wal majdi a haqqu ma kalal abdi wa kulluna laka abdi Allahumma la ma ni’a lima a’adaita wa la mu’udi lima mana’ata wa la yanfa’u zal jadd minkal jadd

Rawi (muslim 477, Abu dawud 747)
·        Rabbana walakalhamdu hamdan kasiran tayiban mubarakan fihi.
Rawi (bukhari 237, Abu dawud 770)
 • Azzikru fissujud (zikiri cikin sujjada)
Allahumma laka sajadtu wa bika a’mantu wa laka  aslamtu sajada wajhi lilazi qalaqahu wa sawwarahu wa shaqqa wa basaruhu tabarakallahu ahsanul qa’liqina.

Rawi (muslim 771)
·        Subhanakallahumma rabbana wa bi hamdika Allahumma agfirli
·        Sauran biyun cikin na ruku’u za a iya yinsu a cikin sujjada (subbuhun quddusun ……………..)
·        (subhana zil jabaruti …………………..)
 • Al’iksaru minad du’a fis sujjud (yawanta yin addu’a a cikin sujjada)
Da cewar sa annabi (SAW) amma a cikin yin sujjada ku yawaita yin addua tabas za a karba muku. Annabi (SAW) ya kasance yana fada a cikin sujjadar sa ‘’Allahumma agfirli zanbi kullahu dikkahu wa jillahu wa awwalahu wa akhirahu wa alaniyyatahu wa sirrahu’’
Rawi muslim 483
 • Addua baina sajadataini
Allahumma agfirli warhamni wajbirni wahdini warzuqni
Rawi (Abu Dawud 850, Tirmizi 284)
·        Rabigfirli Rabigfirli
Rawi (Abu Dawud 874)
 • Assalatu ala nabiyyi ba’ada tashahudu auwal wal akhir (yi wa annabi salatu bayan tahiyar farko da na karshe)
RA’AYOYIN MALLAMAI
 • Imam shafi’i da imam Ahmad sun tafi akan wajabci yi wa annabi sallati a tahiyar karshe. Da mutum zai bari bai yi sallah sa bai inganta ba. Dan cewar sa annabi (SAW) acikin hadisin da hakim da abu hatim suka rawaito acikin sahihansu (yaya za mu yi maka sallati acikin sallah).
 • Imam abu hanifa da malik sun tafi akan cewa yi wa annabi sallati a tahiyar karshe sunnah ne. dan cewar sa annabi (SAW) bayan ya koyar da yanda za a yi tahiya sai yace idan ku ka aikata haka sallah ku ta cika. (wannan shine dalilin su cewar yin sallati acikin sallah sunnah ne).
TUNATARWA
Amma ra’ayin mallaman farko (Imam shafi’i da Imam Ahmad shine       mafi rinjaye )
Ga daya daga cikin salatin Annabi (SAW)
Allahumma salli ala Muhammad wa ala ali Muhammad wa barik ala Muhammad wa ala ali Muhammad kama barakta ala Ibrahim wa ala ali Ibrahim innaka hamidun majid
 • Addua ba’adu tashahud auwal wa tsani (yin addua bayan tahiyar farko da ta karshe)
Amma yin addua a tahiyar farko dan cewar annabi (SAW) idan kunyi zama acikin kowane raka’a biyu ku ce (attahiya’atu lillah ………………………) sannan dayanku ya yi zabi da addua da yake so, amma bayan tahiya ta biyu dan cewar sa annabi (SAW) idan dayanku ya gama tahiya karshe ya nemi tsari daga wajen Allah akan abubuwa guda hudu;

·        Min azabi jahannam (neman tsari daga azaban wuta)
·        Min azabi kabari (neman tsari dage azaban kabari)
·        Wa min fitnatil mahya wal mamat (neman tsari daga fitina rayuwa da mutuwa)
·        Wa min sharri masihi dajjal (neman tsari daga sharin dajjal)
Rawi (bukhari 192, muslim 588)
 • Attaslimatu tsaniya (yin sallama ta biyu)
Hakika annabi (SAW) ya kasance yana sallama biyu. An samo hadisin daga A’mir bin Sa’ad daga babansa y ace ni na ga annabi (SAW) yana sallama a gefen dama da gefen hagu har ina ganin hasken kumatun sa. (muslim 582).
Ita kuma sallama ta farko wajibi ce ta biyu kuma sunnah ce. Ya tabbata annabi (SAW) yana yin sallama kwaya daya. Aisha uwar muminai ta ce lallai annabi (SAW) ya kasance yana sallama daya acikin sallah ta gabar fuskar sa sannan sai ya karkata zuwa gefen dama kadan.
Rawi (Tirmizi 290)
                                    TUNATARWA
Amma mallamai sun ce yana yin sallama dayanne a sallah nafila a gida wannan shi ya kawo uwar muminai ta gani har ta fada. Amma maganar yin sallama biyu shine mafi ingancin zance wanda sahabai sama da goma sha biyar suka kawo riwayar. Ga sunnan su kamar haka;

1)  Abdullahi bin mas’ud
2)  Sa’ad bin Abi waqqas
3)  Sahal bin Sa’ad assa’idi
4)  Wa’il bi hujirin
5)   Abu musa alshari
6)   Khuzaifatul yamani
7)   Ammaru bin yasir
8)   Abdullahi bin Umar
9)   Jabir bin samura
10) Barra’u bin azib
11) Abu maliki ashari
12) Dalk bin aliyu
13) Aus bin Aus
14) Abu ramsa
15) Adiyu bin umaira

Ku duba littafin zadul ma’ad fi hadiyi khairul ibad na ibn qayim aljauziya mujjaladi na daya shafi na shasa’in da tara zuwa dari.
 • Azzikr wa du’a ba’ada sallah (zikiri da addua bayan sallah)
Yin zikiri a bayan sallah ya tabbata cikin hadisai da dama daga cikinsu:
·        Duk wanda yayi subhanallah 33 alhamdulillah 33 allahu akbar 33 a karshen sallah ya cika ya cike na dari da cewa la’ilaha ilallah wahdahu la sharika lahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shay’in kadir. Annabi (SAW) yace za a kankare zunuban sa ko sun kai yawan kumfar teku
Rawi (muslim 597)
·        Annabi (SAW) ya kasance idan ya idar da sallah yana cewa astagfirullah sau 3 allahumma anta sallam wa minka sallam tabarakta ya zal jalali wal ikram
·        An samo daga ukbar bin a’mir annabi (SAW) ya umarce ni ina karanta  falaki da nasi karshen ko wace sallah
Rawi (Abu dawud 1523)
·        Wanda duk ya karanta ayatul kursiyyu a karshen ko wace sallah ta wajibi ba abinda zai hana shi shiga aljannah sai mutuwa
Rawi (Ibn sinni)
Amma addua bayan sallah suna da yawa amma ga daya daga cikin su; (allahumma a’ini zikirika wa shukrika wa husni ibadatik)
Rawi (Abu dawud 1508)


MARKAZ NA SALAFIYYA NGURU YOBE STATE MALLAM IDRIS IBRAHIM ASSALAFI NGURU (SHUGABAN MARKAZ)

DUA’UL ISTIFTAH ADDUAR BUDE SALLAH

DUA’UL ISTIFTAH (ADDUAR BUDE SALLAH)
SIGOGIN
1)      HADISIN ABU HURAIRAH
Allahumma baïd baini wa baina khadayaya kama ba adta bainal mashriki wal magrib, allahumma naqhini min khadayaya kama yunaqha saubul abyadu minaddanasi, allahumma igsilni min khadayaya bilmai wassalji wal baradi.
Masu riwayar hadisin
·        Bukhari 784
·        Muslim 598

2)      HADISIN ABDULLAHI IBN UMAR
Allahu akbar kabiran, walhamdulilahi kasiran, wa subhanallahi bukratan wa asila.
Masu riwayar hadisin
·        Muslim 601
·        Tirmizi 3592

3)      HADISIN AISHA UWAR MUMINAI (R.A.H) DA ABU SAIDUL KHUDRI (R.A.)
Subhanaka Allahumma wa bi hamdika  wa tabarka ismuka wa ta’ala jadduka wa la ilaha ghairuka.
Masu riwayar hadisin
·        Abu Dawud 776
·        Tirmizi 243
·        Ibnu ma’ja 706

4)      HADISIN ALIYU (R.A)
Wajjahtu wajhi lilladhi fadarassamawati wal ardi hanifan wama ana minal mushrikina, inna salati wa nusuki wa mahyaya wa mamati lillahi rabbil aalamina la sharika lahu wabi zalika umirtu wa ana auwalul muslimina, Allahumma antal maliku la ilaha illa anta, anta rabbi waána abduka zalamtu nafsi, wa aátaraftu bizanbi fagfili zunubi ja mian innahu la yagfiruzzunuba illa anta wahdini li ahsamil akhlaaki layahdi li ahsamiha illa anta, wasrif anni sayyi iha, la yasrif anni sayyi iha illa anta. Labbaika wa saadaika wal khairu kulluhu biyadaika, washsharru laisa ilaika ana bika wa ilaika tabaarakta wataálaita astagfiruka wa atuubu ilaika.

Masu riwayar hadisin
·        Muslim 771
·        Abu Dawud 760
·        Tirmizi 342
TUNATARWA
Wannan adduar ta bude sallah, Annabi S.A.W. yafi yinta a sallar dare ta nafila.

5)      HADISIN AISHA UWAR MUMINAI
Allahumma rabba jibrilu wa mikaílu wa israfilu, fadirassamawati wal ardi, aalimil ghaibi wash shahada anta tahkumu baina ibaadika fima kanu fihi yakhtalifuna, ihdini limah uktulifa fihi minal hakka bi iznika innaka tahdi man tasha ila siratimmustaqeem.
Mai riwayar hadisin
·        Muslim 770
TUNATARWA
Manyan magabata kamar Sauri, Ahmad da ishaq sunyi amfani da hadisin ibn Umar, Aisha, Abi Saidul Kudri, Imam Shafai da hadisin Aliyyu (R.A).
Amma imam Malik rahimahullah bai kawo shar’ancin yin dua’ul istiftah, istiaazatu, basmala a farkon sallah ba.
Ma’ana: bai daukeshi yanda sauran magabata suka fahimta ba.
Allahu aalam. Amma abunda yazo cikin nassi dashi ake amfani. Shar’ancin yin shine abunda ya tabbata.
Ka/ki duba littafin al’ausad V3 Page 86, al’mudawwana V1 Page 63
Abunso ne ashar’ance ana yin kowace seega ta wannan addua (suna nan da yawa, wannan kadan ne muka kawo).

MARKAZ NA SALAFIYYA NGURU YOBE STATE MALLAM IDRIS IBRAHIM ASSALAFI NGURU (SHUGABAN MARKAZ)

Thursday, August 18, 2011

JADAWALIN ALFIJIR DANA SHAN RUWA RAMADAN 2011

Jadawalin Alfijir dana Shan Ruwa
(Ramadan 2011)
Wannan lokutan ya shafi jihar Kano
ne da wasu garuruwanta kamar Kachako sai wasu bangarori na Jihohin
Jigawa, Katsina da Kaduna kawai,
za'a iya samu kari ko ragi a wasu
jihohin dake nesa da Kano, kamar
Nasarawa +5 Lagos +20 Kebbi +18
Zamfara +17 Yobe -14 Bauchi -4
Taraba -10 Jos -4 Maiduguri -19 da
sauransu.
Ga lokutan kamar haka:-
Alfijir === Shan Ruwa
1. 4:58am = 6:52pm
2. 4:58am = 6:51pm
3. 4:58am = 6:51pm
4. 4:58am = 6:51pm
5. 4:59am = 6:50pm
6. 4:59am = 6:50pm
7. 4:59am = 6:50pm
8. 5:00am = 6:49pm
9. 5:00am = 6:49pm
10. 5:00am = 6:48pm
11. 5:00am = 6:48pm
12. 5:01am = 6:47pm
13. 5:01am = 6:47pm
14. 5:01am = 6:47pm
15. 5:01am = 6:46pm
16. 5:02am = 6:46pm
17. 5:02am = 6:45pm
18. 5:02am = 6:45pm
19. 5:02am = 6:44pm
20. 5:02am = 6:43pm
21. 5:03am = 6:43pm
22. 5:03am = 6:42pm
23. 5:03am = 6:42pm
24. 5:03am = 6:41pm
25. 5:03am = 6:41pm
26. 5:03am = 6:40pm
27. 5:04am = 6:39pm
28. 5:04am = 6:39pm
29. 5:04am = 6:38pm
Allah ya karbi Ibadunmu, kuma
karmu manta da yiwa juna addu'a
ta gari, gami da kasarmu Nigeria
baki daya.

Friday, July 29, 2011

TABA KIDI TABA KARATUTABA KIDI TABA KARATU

Wata budurwa ce a kullum idan aka zo
aurar da wata ’yar uwarta budurwa, sai ta ji ana ce mata ta yi hakuri, da sauran irin fadan nan na jan kunne da ake wa amare. Ashe abin yana damun wannan budurwa. Rannan sai ta fce: "Ni fa idan aurena ya zo, kada wanda ya ba ni hakuri, domin ba ma zan yi hakurin ba. Idan na tashi zaben miji, dan karamin mutum zan aura, mara karfi. Duk lokacin da ya yi mini ba daidai ba in casa shi kawai!"


Qaqa za mu haxu?
Wani Buzu ne rannan ba shi da ko
kwabo a aljihu, kuma ga shi yana
matuqar jin yunwa, sai ya ga wata yarinya mai sayar da shinkafa, ya kira ta, ya ce ta zuba masa ta Naira hamsin. Bayan ta zuba masa ya cinye, ta tambayi kuxinta sai ya ce mata ta je talla, idan ta dawo sai ya ba ta. Ita kuwa yarinya ta ce ba ta nan za ta dawo ba. Shi kuwa ya ce mata lallai sai dai ta dawo domin a lokacin bai da ko kwabo. Jin haka sai yarinyar nan ta ce: "Idan har ba za ka ba ni kuxina ba, zan bar ka da Allah, mun haxu a lahira." Jin haka sai Buzun nan ya ce: "Ke wagga yarinya, ki daina wanga batu, ke da kika mutuwa a Najeriya, ni da naka mutuwa a Nijar, shin ta qaqa za mu haxu a lahira?


Tusar Bature
Wani Banufe ne yana tuka wani Bature, kullum sai Banufen nan yana cikin tuki sai Baturen nan ya karkace ya saki tusa, da sun hada ido sai ya ce wa Banufe “Sorry, sorry (yi hakuri).” Da ma tusar ba wari gare ta ba, tun da shayi ne da ganye abincinsa. Da Banufe ya ji haushi sai ya dauki alkawarin sai ya rama cin mutuncin da ubangidansa Bature yake yi masa. Rannan ana ba shi albashin tukin da yake yi sai ya tafi kasuwa ya sawo albasa mai yawa, ya ce wa matarsa ta yi masa shaye-shaye da romo, wato dafaffar albasa da miyar kuli-kuli. Bayan ya ci ya koshi, don ko abincin dare bai ci ba sai albasa. Kafin gari ya waye, cikin Banufe ya tsumama, yana fara tuka motar ke nan; tun kafin Bature ya fara yin tusa, sai Banufe ya karkace ya saki tusa. Ya waiga ya ce wa Bature “Sorry sir (yi hakuri yallabai).” Bature ya gyada kai, ya dan sauke gilasan motar yadda iska za ta shigo. Ba a dade ba, Banufe ya sake sakin wata tusar, Bature ya ji warin ya yi yawa, ya bude gilasan motar dukkansu. Ya dauko turare ya fesa, amma dai warin yana nan. Banufe ya waigo ya ce “Sorry sir (yi hakuri yallabai).” Bature ya yi banza da shi. Shi kuwa bai bari warin waccan tusar ya gama fita ba, ya sake sakin wata da karfi. Ya waigo zai ba ubangidansa hakuri ke nan sai Baturen ya ce, “Ah! You want kill me? (Kana son kashe ni ne)?” Banufe ya fashe da dariyar mugunta ya ce “Oga, I will not kill you but... (Oga, ba zan kashe ka ba, amma…)” Tun kafin ya gama yi masa bayani, Baturen ya daka masa tsawa, ya ce “Wait, wait.” Banufe bai gama tsayawa ba, Bature ya sauka daga motar. Bai koma cikin motar ba sai da warin tusar ya gama fita sannan ya shiga suka tafi. Tun daga ranar Bature ya daina yi wa Banufe tusa a cikin mota

Saturday, June 25, 2011

JUMA'AT KAREEM

Haqiqa;
Mafi Girman Haske-Ilimi.
Mafi Girman Duhu-Jahilci
Mafi Girman Kyauta-Afuwa
Mafi Kyawon Zance-Gaskiya
Mafi Munin Zance-Karya
Mafi Kusantowar Al'amari- Tashin Qiyama
Mafi Girman Arziki- Wadatar Zuci
Mafi Kyawun Hali-Kunya
Mafi Munin Hali-Kisan Kai
Mafi Kusanta ga Allah- Ibada
Mafi Kusanta ga Shaidan- Hassada
Mafi Kusanta ga Aljanna- Aikin Alkhairi
Mafi Kusanta ga Wuta- Aikata Sharri. Allah yasa mufi karfin Zukatammu.

MAKIRCIN SHAIDAN GA DANADAM (2)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai
jinkai. Dukkan yabo da godiya na
Allah ne, Ubangijin halittu. Tsira da
amincin Allah su tabbata ga
mafificin halittu, Muhammadu dan
Abdullahi, sallallahu alaihi wasallam, tare da alayensa da
sahabbansa da duk wanda ya bi
tafarkinsu har zuwa ranar karshe.
Bayan haka, yau ga ci gaban
tattaunawar Manzon Allah,
sallallaahu alaihi wasallam da shaidan. Mun kwana daidai inda
Ma’aiki, sallallaahu alaihi wasallam, ya yi godiya ga Allah da Ya azurta
al’ummarsa kuma ya tsiyata shaidan. Daga nan:
Sai Iblis ya ce, “ba mai yiyuwa ba ne. Ina ka ga tsirar al’ummarka alhali ni ina raye zuwa lokaci abin
sani? Yaya za ka dinga farin ciki a
kan al’ummarka, alhali ni ina mai shiga cikin jikinsu da magudanar
jininsu da tsoka, kuma alhali su ba
sa ganina. Kai, wallahi na rantse da
Wanda Ya halicce ni kuma Ya
jinkirta min zuwa ranar tashi, sai na
hallakar da su gabaki dayan su. Jahilansu da malamansu. Wadanda
suka iya karatu da wadanda ba su
iya karatu ba. Da kuma masu bautar
Ubangiji, sai dai bayin Ubangiji
tsarkakakku. ” Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to su wane ne tsarkakakku a wajen ka ?” Sai shaidan ya ce, “ya Muhammadu, yanzu ba ka san cewa duk wanda
yake kaunar duniya da dukiya ba ya
cikin tsarkakakkun bayin Allah
Madaukaki ba? Amma idan ka ga
mutum ba ya kaunar duniya, ba ya
kaunar dukiya kuma ba ya kaunar yabo balle a yabe shi, to hakika na
san wannan yana daga cikin bayin
Allah tsarkakakku. To wannan sai na
rabu da shi domin ya fi karfina.
Hakika idan bawa ya dawwama a
kan son dukiya da son a yabe shi kuma zuciyarsa ta ta’allaka sha’awe-sha’awen duniya, to hakika shi wannan ya tattare dukkan abin
da na siffanta maku.
“ Yanzu ya Muhammadu, ba ka san son dukiya na daga cikin manya-
manyan zunubai ba? Yanzu ya
Muhammadu, ba ka san cewa son
shugabanci yana daga cikin manya-
manyan zunubai ba? Ya
Muhammadu, ba ka san cewa ni ina da ’ya’ya dubu saba’in ba? Kuma kowane daya daga cikinsu yana da
rundunar shaidanu guda dubu
saba’in a karkashinsa? Akwai daga cikinsu wanda na
wakilta shi a kan tsofaffi, amma
matasa kuwa babu wani sabani
tsakanina da su. Amma kananan
yara kuwa sai shaidanu su dinga
wasa da su kamar yadda suka ga dama. Akwai daga cikinsu wanda
hakika na wakilta shi ga masu
bautar Ubangiji. Akwai daga cikinsu
wanda na wakilta shi ga masu
gudun duniya, suna kaiwa suna
komowa a tsakaninsu, kuma suna fitar da su daga wannan hali zuwa
wancan hali, daga wannan kofar
zuwa waccan kofar, har sai sun fitar
da su daga hanyoyi zuwa wadansu
hanyoyi. Ni kuma sai na bata musu
tsarkin aikinsu, alhali suna masu bautar Allah Madaukaki ba tare da
tsarkakewar aiki ba, alhali kuma su
ba su sani ba.
“ Yanzu ya Muhammadu, ba ka da labarin Barsisi mai ibada cikin
addinin Nasara, wanda ya shafe
shekara saba’in [70] yana tsarkake aikinsa saboda Ubangiji Madaukaki,
har sai da ta kai Allah Ya warkar da
marasa lafiya da addu’arsa, amma ban bar shi ya kai ba. Sai da na sa
shi ya yi zina kuma ya yi kisan kai,
kuma ya zama kafiri. Ai shi ne
wanda Ubangiji Ya ambace shi a
cikin Littafinsa Mabuwayi da fadinSa
cewa: ‘Cewar misalin shaidan ne a yayin da ya ce da dan Adam
kafirce’. A lokacin da ya kafirce, sai shaidan ya ce da shi. ‘To ni babu ni, babu kai, domin ni ina tsoron Allah,
Ubangijin halittu”. “Yanzu ya Muhammadu, ba ka san cewa dukkan karya daga gare ni
take ba? Kuma ni ne wanda ya fara
yin karya? Kuma ni ba ni da aboki
sai makaryaci, wanda ya yi
rantsuwar karya, to shi ne
masoyina. “ Ya Muhammadu, yanzu ba ka san ni ne wanda ya rantse wa Hauwa’u da Adamu da Allah a kan cewa ni
mai nasiha ne a gare su ba ? Kuma
rantsuwar karya ita ce take faranta
min zuciya. Giba da annamimanci
kuwa su ne kayan marmarina da
farin cikina. Shaidar karya kuwa ita ce sanyin idanuwana, kuma ita ce
abar yardata. Wanda ya yi
rantsuwar shirka kuwa to ya
kusanta, ya zama babban mai
zunubi ko da rantsuwar shirkar nan
sau daya ne kawai, kuma ko da gaskiya ya fada, domin kuwa
wanda ya saba wa harshensa da
rantsuwar shirka, to hakika an
haramta masa matarsa. Sannan
kuma ba za su gushe ba suna
mazinata, kuma suna hayyafa har zuwa ranar Alkiyama, sai sun
kasance ’ya’yan zina gabaki dayansu. Sai a shigar da su wuta
saboda kalma kwaya daya tak.
“ Ya Muhammadu, hakika daga cikin al’ummarka akwai wanda yake jinkirta sallah daga lokacinta zuwa
wani lokacin. A duk yayin da yake
so ya mike zuwa sallah sai na tsare
shi ina yi masa waswasi, kuma sai
na ce da shi ‘akwai sauran lokaci, ba ka karasa abin da yake gabanka ba ’, har dai ya jinkirta sallah ya yi ta ba
a kan lokacinta ba. Sai a nannade
masa sallarsa a maka masa ita a
fuskarsa. Idan na ga zai rinjaye ni,
ya yi ta a kan lokacinta, sai na aiko
masa da wani daga cikin shaidanun mutane, sai ya shagaltar da shi har
lokacinta ya wuce. Idan kuma ya
rijaye ni a kan wannan, sai na kyale
shi har sai ya fara yin sallar, sai na
dinga cewa da shi ‘dubi hagu, dubi dama’, to idan na ga haka, sai raina ya yi mini dadi, sai na shafi fuskarsa
kuma na tsotsi tsakanin idanunsa
sai na dinga cewa yanzu ka aikata
abin da har abada sallarka ba za ta
gyaru ba’. “Kuma ka sani, ya Muhammadu, wanda ya yi waiwaye a cikin
sallarsa, to Ubangiji zai sa a mako
masa sallarsa a fuska. Idan kuwa ya
rinjaye ni a cikin sallarsa ya zo ya yi
ta shi kadai, to sai na sa shi ya yi ta
a cikin gaggawa sai ya dinga dungura ta kamar yadda zakara
yake tsattsagar dawa, nan da nan
kamar koton kurciya. Idan kuwa ya
rinjaye ni har na ga zai yi sallah a
cikin jama’a, to ba kyale shi zan yi ba. Sai na daura masa linzami. Ina
mai daga kansa kafin liman ya
daga. Kuma ina mai sunkuyar da
kansa kafin liman ya sunkuya. Kai
kuma ka sani, ya Muhammadu, duk
wanda ya aikata haka to ba shi da sallah. Idan kuma ya rinjaye ni a
nan, to sai na umarce shi ya dinga
tantankwasa hannunsa alhali yana
cikin sallar. Wanda ya aikata haka
kuwa, ni yake yi wa tasbihi a cikin
sallarsa. Idan kuwa ya rinjaye ni a nan, to sai na yi masa busa a cikin
hancinsa, wacce take za ta sa shi ya
yi hamma a cikin sallarsa, idan bai
toshe bakinsa a yayin da yake
hammar ba, to sai in shiga cikin
bakinsa. To wannan sai ya kara masa son duniya da kaunarta. Sai
ya kasance ba ya sauraren kowa sai
ni, kuma ba ya biyayya ga kowa sai
ni.
“ Ya Muhammadu, ina aikin al’ummar taka yake? Ga ni ina umarnin talakawa, ina ce musu
sallah ba ta talakawa ba ce, ta
wadanda Allah Ya yi wa ni’ima ce. Kuma ina cewa da marar lafiya,
sallah ba wajibi ba ce a kan marasa
lafiya, sallah ta wadanda Allah Ya yi
wa ni’ima da lafiya ce. Ba ku ji Ubangiji Madaukaki yana cewa:
“Babu laifi ga marar lafiya” , idan kuwa sallah ta kubuce ma marar
lafiya har ya mutu, to hakika ya
mutu kafiri, idan kuwa ya mutu
yana tarikus-salat a yayin rashin
lafiyarsa to hakika zai sadu da
Ubangiji Yana mai fushi da shi. “ Ya Muhammadu, idan abubuwan da nake gaya maka karya ne, to roki
Ubangiji Ya maida ni toka. Ya
Muhammadu, yaya za ka yi farin ciki
a kan al’ummarka, alhali na kasance ina fitar da sudusin al’ummarka daga Musulunci?” Sai Manzon Allah SAW ya ce, “ya kai la’antaccen Allah, wane ne abokin zaman ka?” Sai shaidan ya ce: “maciyin riba shi ne abokin zamana.” Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to wane ne abokinka?” Sai shaidan ya ce “barawo shi ne abokina.” Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to wane ne masoyinka?” Sai shaidan ya ce, “Tarikus-Salat (wato mai barin sallah) shi ne
masoyina.” Sai Manzon Allah SAW ya ce, “ya la’antaccen Allah, to mene ne yake karya doron bayanka?” Sai shaidan ya ce, “kururuwar doki a wajen daukaka kalmar Allah. ” Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to mene ne yake narkar da jininka ?” Sai shaidan ya ce, “tuban mai tuba, shi ne yake narkar da ni.”