Sunnonin da aka aikata su da gabbai
1) ITTIKHA’ZUL SITRU FISSALATI (SANYA SUTRA ACIKIN YIN SALLAH)
Sunna ne akkan massala’ta su sanya sutra a gabansa dan kare abin da ze gifta a gabansa dan cewarsa annabi (SAW) idan dayanku zai yi sallah ya sanya sutra ya kusance ta shaitani ba zai yanke mar sallah ba. Rawi (Abu Dawud 681)
a. Ya tabbata daga annabi (SAW) ya kasance yana daga hannayensa wani lokaci taren da yin kabbara.
b. Wani lokacin kuma bayan yin kabbara
c. Wani lokacin kuma kafin yin kabbara
3) WAD’UL YUMNA ALAL YUSRA FAUKASSADRI (DAURAN HANNUN DAMA AKAN HANNUN HAGU AKAN KIRJI)
a) An samo hadisin daga Sahal bin Sa’ad ya ce mutane sun kasance ana ba’su umarni akan su daura hannayensu na dama akan zira’i hannun hagu acikin sallah. Rawi (Bukhari 740, Malik Muatta 376).
b) An samo hadisin daga Wa’il bin Hujirin yace na yi sallah tare da annabi (SAW) sai ya daura hannunsa na dama akan na hagu akan kirjinsa acikin sallah. Rawi (ibn khuzaima 479) Albani ya inganta wannan hadisin a littafinsa irwa’ul ghalil 352
4) ANNAZRU MUHALLISSUJUD (KALLON GURIN SA GOSHI) Aisha uwar muminai ta ce yayin da Annabi (SAW) shiga ka’aba idonsa bai saba wa kallon gurin sujjadassa ba ma’ana idonsa yana kallon inda goshinsa yake tabawa Rawi (Alhakim 479)
5) ISTIWA’UZZAHR FIRRUKU’U WA ADAMU RAF’URRASI AU KHAFDUHU WAL QABDU BIL KAFFI ALARRUKUBATAINI MA’ATAFRIJUL ASABI’I WAMUBAADATUL ADUDAINI ANIL JAMBAINI (DAIDAITA GADON BAYA ACIKIN RUKU’U KADA A DAGA KAI SAMA KAR A KWANTAR DA SHI CHAN KASA DA BUDA TAFIKAN HANNU A DANKI GUIWA DA SU DA NISANTAR DA MANNE HANNAYE GUDA BIYU ACIKIN JIKI).
a. Saboda hadisin Abi Humaid acikin irin siffar sallah annabi (SAW) idan ya yi ruku’u yana daura hannayensa akan guiwowinsa sannan ya mike gadon bayansa har sai ya zama ya daidaita shi bai karkata ba. Rawi (Bukhari 821, Abu Dawud 717). b. Hadisin uwar muminai ta ce annabi (SAW) ya kasance in ya yi ruku’u baya daga kansa sama sai dai yana daidaitawa sakani. Rawi (Muslim 498, Abu Dawud 768)
1) ITTIKHA’ZUL SITRU FISSALATI (SANYA SUTRA ACIKIN YIN SALLAH)
Sunna ne akkan massala’ta su sanya sutra a gabansa dan kare abin da ze gifta a gabansa dan cewarsa annabi (SAW) idan dayanku zai yi sallah ya sanya sutra ya kusance ta shaitani ba zai yanke mar sallah ba. Rawi (Abu Dawud 681)
TANBIHI (TUNATARWA)
Wannan sutra da muka ambata ko wani bango ko abin dogara ko wata sanda da za a iya kafa koma me ma za a iya sitra da su. Ko misali karshen sirdi na abin hawa
Da kuma cewarsa annabi (SAW) idan dayanku ya sanya a gabansa sitra kamar misali karshen sirdi na abun hawa babu damuwa kan mai wucewa ta gabansa
Rawi (Muslim 499, Tirmizi 33)
2) Raf’ul yadaini inda takbiratul ihram wa indarruku’i warraf’u minhu wa indal qiyami minattashahuddil auwal wa kazalika inda kulli raf’in wa qafdin (daga hannaye guda biyu a yin kabara harama da lokaci yin ruku’u da dagowa daga ruku’u da tashi bayan gama tahiyar farko haka a dukkan dagowa da tafiya)
An samo hadisin daga Nafi’i yace Abdullahi dan Umar ya kasance idan zai shiga cikin sallah yana yin kabbara yana daga hannayensa idan zai yi ruku’u ma yana daga hannayensa, idan yace samiallahu liman hamidahu yana daga hannayensa sannan idan ya dago daga raka’a ta biyu yana daga hannayensa. Abdullahi dan Umar ya mika wannan Magana cewa daga wajen annabi ya’ga yanayin haka.
Rawi (Bukhari 739, Muslim 504)
TANBIHI (TUNATARWA)
Wadannan gurare guda hudu da muka ambata cikin wannan hadisin su ne inda karfafa daga hannaye sai dai sunnah ne wani lokaci (ahyanan) daga hannaye a ko wace dagowa ko tafiya saboda hadisin da aka samu daga Maliku ibnul Huwairis lallai shi ya ga annabi da idonsa yana daga hannayensa idan zai yi ruku’u kuma yana daga hannayensa idan zai dago daga ruku’u idan zai tafi sujjada haka idan zai dago daga sujjada, yana daga hannayensa kusa da kunnuwansa.
Rawi (Nasa’i vol. 2 hadiths 206)
MUHALLURRAF’I WA SIFFATIHI (WAJAJEN DAGA HANNU DA YADDA AKE YI)