Muna Murna Da Ziyarar Da Aka Kawo Mana

Muna Godiya Da Farin Ciki Ga Duk Gudun Mawar Shawara Dag Zaku Iya Bamu,

Sai Munji Daga Gare ku.

Friday, July 29, 2011

TABA KIDI TABA KARATUTABA KIDI TABA KARATU

Wata budurwa ce a kullum idan aka zo
aurar da wata ’yar uwarta budurwa, sai ta ji ana ce mata ta yi hakuri, da sauran irin fadan nan na jan kunne da ake wa amare. Ashe abin yana damun wannan budurwa. Rannan sai ta fce: "Ni fa idan aurena ya zo, kada wanda ya ba ni hakuri, domin ba ma zan yi hakurin ba. Idan na tashi zaben miji, dan karamin mutum zan aura, mara karfi. Duk lokacin da ya yi mini ba daidai ba in casa shi kawai!"


Qaqa za mu haxu?
Wani Buzu ne rannan ba shi da ko
kwabo a aljihu, kuma ga shi yana
matuqar jin yunwa, sai ya ga wata yarinya mai sayar da shinkafa, ya kira ta, ya ce ta zuba masa ta Naira hamsin. Bayan ta zuba masa ya cinye, ta tambayi kuxinta sai ya ce mata ta je talla, idan ta dawo sai ya ba ta. Ita kuwa yarinya ta ce ba ta nan za ta dawo ba. Shi kuwa ya ce mata lallai sai dai ta dawo domin a lokacin bai da ko kwabo. Jin haka sai yarinyar nan ta ce: "Idan har ba za ka ba ni kuxina ba, zan bar ka da Allah, mun haxu a lahira." Jin haka sai Buzun nan ya ce: "Ke wagga yarinya, ki daina wanga batu, ke da kika mutuwa a Najeriya, ni da naka mutuwa a Nijar, shin ta qaqa za mu haxu a lahira?


Tusar Bature
Wani Banufe ne yana tuka wani Bature, kullum sai Banufen nan yana cikin tuki sai Baturen nan ya karkace ya saki tusa, da sun hada ido sai ya ce wa Banufe “Sorry, sorry (yi hakuri).” Da ma tusar ba wari gare ta ba, tun da shayi ne da ganye abincinsa. Da Banufe ya ji haushi sai ya dauki alkawarin sai ya rama cin mutuncin da ubangidansa Bature yake yi masa. Rannan ana ba shi albashin tukin da yake yi sai ya tafi kasuwa ya sawo albasa mai yawa, ya ce wa matarsa ta yi masa shaye-shaye da romo, wato dafaffar albasa da miyar kuli-kuli. Bayan ya ci ya koshi, don ko abincin dare bai ci ba sai albasa. Kafin gari ya waye, cikin Banufe ya tsumama, yana fara tuka motar ke nan; tun kafin Bature ya fara yin tusa, sai Banufe ya karkace ya saki tusa. Ya waiga ya ce wa Bature “Sorry sir (yi hakuri yallabai).” Bature ya gyada kai, ya dan sauke gilasan motar yadda iska za ta shigo. Ba a dade ba, Banufe ya sake sakin wata tusar, Bature ya ji warin ya yi yawa, ya bude gilasan motar dukkansu. Ya dauko turare ya fesa, amma dai warin yana nan. Banufe ya waigo ya ce “Sorry sir (yi hakuri yallabai).” Bature ya yi banza da shi. Shi kuwa bai bari warin waccan tusar ya gama fita ba, ya sake sakin wata da karfi. Ya waigo zai ba ubangidansa hakuri ke nan sai Baturen ya ce, “Ah! You want kill me? (Kana son kashe ni ne)?” Banufe ya fashe da dariyar mugunta ya ce “Oga, I will not kill you but... (Oga, ba zan kashe ka ba, amma…)” Tun kafin ya gama yi masa bayani, Baturen ya daka masa tsawa, ya ce “Wait, wait.” Banufe bai gama tsayawa ba, Bature ya sauka daga motar. Bai koma cikin motar ba sai da warin tusar ya gama fita sannan ya shiga suka tafi. Tun daga ranar Bature ya daina yi wa Banufe tusa a cikin mota

No comments:

Post a Comment