Muna Murna Da Ziyarar Da Aka Kawo Mana

Muna Godiya Da Farin Ciki Ga Duk Gudun Mawar Shawara Dag Zaku Iya Bamu,

Sai Munji Daga Gare ku.

Friday, June 5, 2015

SUNNONIN SALLAH

Sun kaso kashi biyu
1.  Sunnonin da za a firta da baki (kauliyya)
2.  Sunnonin da za a aikata da gabbai (fi’íliyya)
Sunnonin da za a firta da ba’ki sun kaso kashi goma
 • Karatun surah bayan fatiha
Sunnah ne karanta surah a rakaóin farko bayan fatiha da ijma’in mallamai (taruwan mallamai) haka kuma sunnah ne karanta surah a raka’oin karshe (raka’ah uku da ta hudu)

DALILI (HUJJA)
Hadisin Abi qata’dah yace manzan Allah (SAW) ya kasance yana karanta a raka’oin farko fatiha da surah yana jiyar da mu ayah wani lokacin yana karantawa a raka’oin biyun karshe da suratul fatiha.
Rawi (muslim 421, bukhari 759).

Amma karantun surah a raka’a  uku da ta hudu an samu ne a hadisin Abi sa’idin lallai  manzan Allah (SAW) ya kasance yana karanta a raka’oin biyun farko na azahar ayoyi talatin talatin sannan a biyun karshe da ayoyi goma sha biyar biyar.
Rawi (muslim 452)
 • Zikiri cikin ruku’u
Allahumma laka raka’atu wa laka aslamtu wa bika a’mantu qhasha’a laka sam’i wa basari wa mukki wa azmi wa asabi
Rawi (muslim 771, tirmizi 4371, Abu dawud 760)
·        Subhanaka Allahumma rabbana wa bi hamdika Allahumma  agfirli
Rawi (bukhari 247, muslim 484)
·        Subbuhun quddusun rabul mala’ikati wa ruhh
Rawi (muslim 487)
·        Subhana zil jabaruti wal malakuti wal kibriya’u wal azma
Rawi (Abu dawud 873)
 • Azikru baádal kiyam minal ruku’i wa ba’ada rabbana walakalhamdu (zikir bayan dagowa daga ruku’u da kuma bayan rabbana walakalhamdu)
Allahumma rabbana walakalhamdu mil’assamawati wa mil’al ardi wa mil’a ma bainahuma wa mil’a ma shita min shay’in baada ahlusana’i wal majdi a haqqu ma kalal abdi wa kulluna laka abdi Allahumma la ma ni’a lima a’adaita wa la mu’udi lima mana’ata wa la yanfa’u zal jadd minkal jadd

Rawi (muslim 477, Abu dawud 747)
·        Rabbana walakalhamdu hamdan kasiran tayiban mubarakan fihi.
Rawi (bukhari 237, Abu dawud 770)
 • Azzikru fissujud (zikiri cikin sujjada)
Allahumma laka sajadtu wa bika a’mantu wa laka  aslamtu sajada wajhi lilazi qalaqahu wa sawwarahu wa shaqqa wa basaruhu tabarakallahu ahsanul qa’liqina.

Rawi (muslim 771)
·        Subhanakallahumma rabbana wa bi hamdika Allahumma agfirli
·        Sauran biyun cikin na ruku’u za a iya yinsu a cikin sujjada (subbuhun quddusun ……………..)
·        (subhana zil jabaruti …………………..)
 • Al’iksaru minad du’a fis sujjud (yawanta yin addu’a a cikin sujjada)
Da cewar sa annabi (SAW) amma a cikin yin sujjada ku yawaita yin addua tabas za a karba muku. Annabi (SAW) ya kasance yana fada a cikin sujjadar sa ‘’Allahumma agfirli zanbi kullahu dikkahu wa jillahu wa awwalahu wa akhirahu wa alaniyyatahu wa sirrahu’’
Rawi muslim 483
 • Addua baina sajadataini
Allahumma agfirli warhamni wajbirni wahdini warzuqni
Rawi (Abu Dawud 850, Tirmizi 284)
·        Rabigfirli Rabigfirli
Rawi (Abu Dawud 874)
 • Assalatu ala nabiyyi ba’ada tashahudu auwal wal akhir (yi wa annabi salatu bayan tahiyar farko da na karshe)
RA’AYOYIN MALLAMAI
 • Imam shafi’i da imam Ahmad sun tafi akan wajabci yi wa annabi sallati a tahiyar karshe. Da mutum zai bari bai yi sallah sa bai inganta ba. Dan cewar sa annabi (SAW) acikin hadisin da hakim da abu hatim suka rawaito acikin sahihansu (yaya za mu yi maka sallati acikin sallah).
 • Imam abu hanifa da malik sun tafi akan cewa yi wa annabi sallati a tahiyar karshe sunnah ne. dan cewar sa annabi (SAW) bayan ya koyar da yanda za a yi tahiya sai yace idan ku ka aikata haka sallah ku ta cika. (wannan shine dalilin su cewar yin sallati acikin sallah sunnah ne).
TUNATARWA
Amma ra’ayin mallaman farko (Imam shafi’i da Imam Ahmad shine       mafi rinjaye )
Ga daya daga cikin salatin Annabi (SAW)
Allahumma salli ala Muhammad wa ala ali Muhammad wa barik ala Muhammad wa ala ali Muhammad kama barakta ala Ibrahim wa ala ali Ibrahim innaka hamidun majid
 • Addua ba’adu tashahud auwal wa tsani (yin addua bayan tahiyar farko da ta karshe)
Amma yin addua a tahiyar farko dan cewar annabi (SAW) idan kunyi zama acikin kowane raka’a biyu ku ce (attahiya’atu lillah ………………………) sannan dayanku ya yi zabi da addua da yake so, amma bayan tahiya ta biyu dan cewar sa annabi (SAW) idan dayanku ya gama tahiya karshe ya nemi tsari daga wajen Allah akan abubuwa guda hudu;

·        Min azabi jahannam (neman tsari daga azaban wuta)
·        Min azabi kabari (neman tsari dage azaban kabari)
·        Wa min fitnatil mahya wal mamat (neman tsari daga fitina rayuwa da mutuwa)
·        Wa min sharri masihi dajjal (neman tsari daga sharin dajjal)
Rawi (bukhari 192, muslim 588)
 • Attaslimatu tsaniya (yin sallama ta biyu)
Hakika annabi (SAW) ya kasance yana sallama biyu. An samo hadisin daga A’mir bin Sa’ad daga babansa y ace ni na ga annabi (SAW) yana sallama a gefen dama da gefen hagu har ina ganin hasken kumatun sa. (muslim 582).
Ita kuma sallama ta farko wajibi ce ta biyu kuma sunnah ce. Ya tabbata annabi (SAW) yana yin sallama kwaya daya. Aisha uwar muminai ta ce lallai annabi (SAW) ya kasance yana sallama daya acikin sallah ta gabar fuskar sa sannan sai ya karkata zuwa gefen dama kadan.
Rawi (Tirmizi 290)
                                    TUNATARWA
Amma mallamai sun ce yana yin sallama dayanne a sallah nafila a gida wannan shi ya kawo uwar muminai ta gani har ta fada. Amma maganar yin sallama biyu shine mafi ingancin zance wanda sahabai sama da goma sha biyar suka kawo riwayar. Ga sunnan su kamar haka;

1)  Abdullahi bin mas’ud
2)  Sa’ad bin Abi waqqas
3)  Sahal bin Sa’ad assa’idi
4)  Wa’il bi hujirin
5)   Abu musa alshari
6)   Khuzaifatul yamani
7)   Ammaru bin yasir
8)   Abdullahi bin Umar
9)   Jabir bin samura
10) Barra’u bin azib
11) Abu maliki ashari
12) Dalk bin aliyu
13) Aus bin Aus
14) Abu ramsa
15) Adiyu bin umaira

Ku duba littafin zadul ma’ad fi hadiyi khairul ibad na ibn qayim aljauziya mujjaladi na daya shafi na shasa’in da tara zuwa dari.
 • Azzikr wa du’a ba’ada sallah (zikiri da addua bayan sallah)
Yin zikiri a bayan sallah ya tabbata cikin hadisai da dama daga cikinsu:
·        Duk wanda yayi subhanallah 33 alhamdulillah 33 allahu akbar 33 a karshen sallah ya cika ya cike na dari da cewa la’ilaha ilallah wahdahu la sharika lahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shay’in kadir. Annabi (SAW) yace za a kankare zunuban sa ko sun kai yawan kumfar teku
Rawi (muslim 597)
·        Annabi (SAW) ya kasance idan ya idar da sallah yana cewa astagfirullah sau 3 allahumma anta sallam wa minka sallam tabarakta ya zal jalali wal ikram
·        An samo daga ukbar bin a’mir annabi (SAW) ya umarce ni ina karanta  falaki da nasi karshen ko wace sallah
Rawi (Abu dawud 1523)
·        Wanda duk ya karanta ayatul kursiyyu a karshen ko wace sallah ta wajibi ba abinda zai hana shi shiga aljannah sai mutuwa
Rawi (Ibn sinni)
Amma addua bayan sallah suna da yawa amma ga daya daga cikin su; (allahumma a’ini zikirika wa shukrika wa husni ibadatik)
Rawi (Abu dawud 1508)


MARKAZ NA SALAFIYYA NGURU YOBE STATE MALLAM IDRIS IBRAHIM ASSALAFI NGURU (SHUGABAN MARKAZ)

No comments:

Post a Comment