Muna Murna Da Ziyarar Da Aka Kawo Mana

Muna Godiya Da Farin Ciki Ga Duk Gudun Mawar Shawara Dag Zaku Iya Bamu,

Sai Munji Daga Gare ku.

Wednesday, June 22, 2011

Ma’ana da illolin zina da luwadi damadigo da kuma hukuncinsu

Ya tabbata a cikin hadisi an tambayi Annabi (S.A.W) a kan wane zunubi ne ya fi girma, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Shirka da Allah alhali Shi ne Ya halicce ka.” Sai aka ce ‘sai wane?’ Sai ya ce, “Sannan kashe danka don kada ya ci tare da kai.” Sai aka ce “sannan sai wane?” Sai ya ce, “Ka yi zina da matar makwabcinka.” (Bukhari).
Allah Madaukakin sarki Ya sanya hukuncin wanda duk ya yi zina kuma ya taba aure, a jefe shi, namiji ko mace; idan kuwa bai taba aure ba, sai a yi masa bulala dari, sannan a bakuntar da shi a wani gari daban tsawon shekara guda.
Duk wanda ya kalli hukuncin zina, zai ga Allah Ya kebance shi da wasu abubuwa masu yawa, saboda munin zina. Ga kadan daga cikin abubuwan da hukuncin ya kunsa:
•Kausasawa wajen ukubar mazinaci, ta hanyar jefewa. Ko kuma bulala da bakuntarwa shekara guda.
•Hana jin tausayin mazinaci ko mazinaciya yayin da ake musu ukuba. Allah Ya ce :
“Mazinaciya da mazinaci ku yi wa kowane daya daga cikinsu bulala dari. Kada ku ji tausayinsu a cikin addinin Allah, in dai kun yi imani da Allah da ranar karshe” . (Annur : 2).
•Yi musu ukuba a gaban mutane, ba a yarda a yi musu a boye ba, Allah Ya ce :
“Wasu bangare na muminai su halarci wajen yi musu ukuba (haddi)”. (Annur :2).
Duk wadannan abubuwa suna nuna mana munin zina da rashin kyanta a Musulunci. Imamul Bukhari ya kawo, a cikin ingantaccen littafinsa, daga Maimun Al-audiy ya ce, “A lokacin jahiliyya na taba ganin wani biri da ya yi zina da wata biranya, sai sauran biran suka taru suka jefe su”.
Mafi munin zina ita ce wadda mutum zai yi da mahaifiyarsa, sai da muharramarsa, sai wadda zai yi da matar makwabcinsa. Allah Ya kare mu.
Illolin Zina: Babu ko shakka duk mai hankali ya san cewa zina tana tattare da illoli masu yawa, wadanda suke shafar mazinacin ko mazinaciyar, ko su shafi al’umma gaba daya. Ga wasu daga cikin illolinta :
1. Zubar da mutunci da jawo wa kai kaskanci: Duk matar da ta yi zina to ta jawo wa kanta da danginta da mijinta kaskanci, ta kuma zubar musu da mutunci a idon duniya. Idan har ta sami ciki ta haihu, sannan ta kashe dan, to ta hada laifi biyu, laifin zina da laifin kisan kai. In kuma ta bar shi, to kuma ta shigar wa mijinta ko danginta, wanda ba ya cikinsu. Idan kuwa mai zinar namiji ne to ya lalata mace, ya jawo mata lalacewa da tabewa, wanda hakan lalata duniya ne
gaba daya.
2. Zina ta hada dukkan sharri gaba daya: Saboda a cikin zina akwai rashin tsoron Allah; rashin kunya; rashin tsantseni; rashin cika alkawari; karya da butulci da sauransu. Duk kuwa wadannan munanan halaye a Musulunci. Ta’aliki: Mukalar kalmomin “Taala” da “Amin” a sallama Daga Alhaji Ahmad Muhammadil’Amin (Bawalle)
Dukkan godiya da yabo suna kara tabbatuwa ga aninihin Mai su, Ubangiji, kuma makagin kowa da komai ALLAH – Tabaraka wata’ala. Mahallicin mutum Ya sanar da shi (mutun) abin da bai sani ba. Dadin tsiran amincin Allah su ci gaba da karuwa ga mafificin halitta, shugaban dukkan Annabawa da Manzanni tare da zuri’arsa tsarkaka bai daya.
A ranar Juma’a 18 ga Muharram 1432, ina ofishina a Ma’ahd, wani dalibi ya zo min da jaridar Aminiya, ya ce “ga jaridar nan, lallai tunda marubucin ya nemi a shiryar da shi, baccin an karanta makalarsa, to ka yi rubutu a kai, kuma wannan maudu’in ya zama shi za ka yi mana ta’liki a ranar Laraba a ma’ahd domin tahdib.” Sai na ce tun da a kan shak’wa ce ilmiyyah, zan rubuta – in Allah (TWT) Ya so - domin na ga shi marubucin na magana ne a kan hujja kuma ai kowa ya san cewa HUJJA MAKAMIN AHLIL – ZIKR ne.
Mai karatu karimi, ina farawa da jawo hankalin duk wanda zai yi jawabi da sunan Musulunci, to, ya yi taka-tsan- tsan, ya ga cewa Zatin Allah ya nufa, kana da tawali’u irin na marubucin a makalarsa. Hujjojinsa su zama daga kitabu, sunnah, babu gociya, baudiya ko kwana, balle fadin son rai don wata manufa tasa, saboda hadarin da ke tattare da yi hakan.
Shi kuma mai hadisi, ijtihadinsa, in ya yi sawaba, ajraini, in kuwa akasin haka, ajrun wahid. Amin. Sai dai na ji dadin fahimtar cewa marubucin makalar ba yana jayayyar daukakar Allah ba ne, ko kuma bai yarda sallama ba fatan alheri ce ba, la la, shi dai a gurinshi ba su da mazauni, gurin yin sallamar ko amsawa. To wannan matsalar ba karama ce ba, tana da fadin gaske, zan raba ta kashi biyu insha’Allah (TWT). Na farko nunasshe da shi cewa duk hujjojinsa na Hadisai 5 ba su tsaya a kan yadda ake yin sallama da mayar da ita kawai ba. Kuma, kamar yadda ya nemi tabbatattun hujjoji na yiwuwar a saka kalmomin, to ga nema a gare shi ta hanyar tambayar - shin in Annabi bai yi ba, yana hukunta cewa kada a yi wani aikin ne? Amsa ita ce, Annabi bai yi ba, ba hujja ba ce, Annabi ya hana, ita ce hujja. Kash, sai ga shi M. Ahmad bai taimaka wa dalibai irinmu da Hadisi
ko da rarruana ne inda Ma’aiki ya hana a ce “Ta’ ala” ko “Amin”, a mas’alar sallama.
Ke nan za mu fahimci cewa yin abu a da’irar Islama yana zama muhdatha ce in har ba ya cikin Ayyukan Islama, amman ko da Annabi bai yi ba, shari’ar Islama ta tabbatar da samun sararin yi a Ayyukan Ibadan.
Misali:- Ingantaccen Hadisin da Imam Muslim ya ruwaito a Kitabus salati, Babu fadlul Duhuri Billail wan-nahar/ wa fadlul Duhuri Ba’dal Wudu’i (Hadith na 1149) da sahihih Muslim Babu Min Fadlul Bilal (Hadith 6,609) inda suka tabbatar cewa Annabi (S.A.W) bai yi wani aiki ba, amman sai ga shi Bila Babban Bawa, ya bai wa Ma’aiki amsa cewa shi a duk lokacin da ya dawwama da tsarki, in har yana da alwala, sai ya yi nafila raka’a biyu. Annabi bai ce masa me ya sa ka yi abin
da ban yi ba, kuma ban sa ka ba. Sai kawai ya tabbatar cewa yana jin motsin takalmin Bilal a gabanshi, a aljanna.

No comments:

Post a Comment