Muna Murna Da Ziyarar Da Aka Kawo Mana

Muna Godiya Da Farin Ciki Ga Duk Gudun Mawar Shawara Dag Zaku Iya Bamu,

Sai Munji Daga Gare ku.

Wednesday, June 22, 2011

MAKIRCIN SHAIDAN GA DAN ADAM

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai
jinkai. Dukkan yabo da godiya na
Allah ne, Ubangijin halittu. Tsira da
amincin Allah su tabbata ga
mafificin halittu, Muhammadu dan
Abdullahi, sallallahu alaihi wasallam, tare da alayensa da
sahabbansa da duk wanda ya bi
tafarkinsu har zuwa ranar karshe.
Bayan haka, a yau da yardar Allah,
ina son yin fadakarwa ne a kan irin
makircin da shaidan ke yi wa dan Adam, a lokacin da yake a raye ko
kuma a lokacin da ya zo mutuwa.
Ya Allah Ka sallada mu a kan
shaidan la’antacce, kuma Ka shiga
tsakaninmu da shi. Amin.
To ya ’yan uwa musulmi, kamar yadda muka sani ne, Allah SWT Ya
ba shaidan damar shiga kowane
bangare na jikin dan Adam, jini da
tsoka da kuma bargo, inda ta kai
har yana lalata imanin mutum, ya
lalata sallar mutum. Yana fitar da kai daga imaninka. Shin mun manta
ne cewa wata rana Allah SWT Ya
taba umartar shaidan da cewa ya je
gurin Manzon Allah, sallallaahu
alaihi wasallam, ya amsa masa
dukkan tambayoyin da zai masa? Abdullahi dan Abbas [RA] ya ce,
“wata rana mun kasance tare da
Manzon Allah, sallallaahu alaihi
wasallam, a cikin wani daya daga
cikin gidajen mutanen Madina, tare
da jama’a, sai muka ji wani mai kira yana kira cewa: “ya ku mutanen
gidan nan ku zo ku yi min iznin
shigowa, domin na tabbata kuna da
bukata a gare ni.” Sai Manzon Allah,
sallallaahu alaihi wasallam, ya ce,
“ko kun san wane ne mai maganar nan?”
Sai sahabbai suka ce, “Allah da
ManzonSa kadai suka sani.” Sai
Annabi ya ce, “Iblis la’antaccen
Allah ne, Allah Ya kara la’antarsa.
Amin.” Sai Umaru dan Khaddabi (RA) ya ce “ya Manzon Allah ko za ka
yi mini izini in kashe shi?” Sai
Manzon Allah, sallallaahu alaihi
wasallam, ya ce “sannu dai ya
Umar, yanzu ba ku san shi shaidan
yana daga cikin wadanda aka saurara wa ba har zuwa lokaci abin
sani? Sai dai ku je ku bude masa
kofa, domin kuwa shi umarninsa
aka yi domin ku fahimci abubuwan
da zai fada muku.”
dan Abbas (RA) ya ce, “sai kuwa aka bude masa. Shigowarsa ke da wuya
sai muka gan shi tsoho ne mai ido
daya, a gemunsa akwai ’yan gasu
irin na doki. Idanunsa kuwa kamar
na alade, labbansa kuwa kamar na
bajimin sa, sai ya ce: ‘Assalamu Alaikum, ya Muhammadu. Assalamu
Alaikum ya jama’atal muslimina’.
Sai Manzon Allah SAW ya ce,
“Aminci ya tabbata ga Allah, ya kai
La’antacce. Kai dai fadi abin da ya
kawo ka da kuma bukatarka.” Sai Iblis ya ce: “ya Muhammadu,
wannan zuwan ba zuwan kaina ba
ne, na zo ne a kan wata bukata.”
Sai Manzon Allah SAW ya ce, “wace
bukata ce ta kawo ka, ya
La’antacce?” Sai Iblis ya ce: “wani mala’aika ya
zo daga Ubangiji Mai Girma, ya ce
‘hakika Ubangiji Madaukaki Yana
umarnin ka da ka je zuwa ga
Muhammadu SAW kana
wulakantacce kuma kana mai kaskastar da kai a gare shi, domin
ka ba shi labarin irin yadda kake
shirya wa dan Adam makirci da
kuma yadda kake hallakar da shi.
Kuma ka gaya masa gaskiya a cikin
duk irin abubuwan da ya tambaye ka. Na rantse da buwayaTa da
daukakaTa, idan ka kuskura ka yi
masa karya guda daya tak, ko kuma
ka ki gaya masa gaskiya, to ka
tabbata Zan kona ka In maida kai
tokar da iska za ta yi dai-dai da ita a bayan kasa. Kuma In sanya
makiyanka su yi maka dariyar
gamgamko.’ To hakika ga ni na zo
maka, ya Muhammadu, kamar
yadda aka umarce ni. Don haka, ya
Muhammadu ka tambayi duk abin da kake so, zan gaya maka gaskiya,
domin idan ban gaya maka gaskiya
ba, to hakika makiyana za su yi mini
dariya. Ni kuma babu abin da na ki
jini a duniya irin dariyar makiyi.”
Manzon Allah SAW ya ce: “Ya Iblis idan ka kasance kai mai gaskiya ne,
to ka ba ni labari wane ne farkon
makiyinka?”
Sai Iblis ya ce, “Muhammadu ai kai
ne babban makiyina a cikin bayin
Allah da kuma duk wanda yake kwaikwayonka Muhammadu.”
Sai Manzon Allah SAW ya ce:
“sannan kuma sai wa ka fi ki Iblis?”
Sai shaidan ya ce, “sai kuma saurayi
mai tsoron Allah, wanda ya mika
kansa wajen bautar Allah Madaukaki.”
Sai Manzon Allah SAW ya ce:
“sannan kuma sai wa?”
Sai Iblis ya ce, “sannan malami mai
tsantseni. Kuma a wani lokaci shi
mai tsoron Allah ne.” Sai Manzon Allah SAW ya ce,
“sannan kuma sai wa ka fi ki?”
Sai Iblis ya ce, “sai malamin da yake
dauwama a cikin tsarki har sau
uku.”
Sai Manzon Allah SAW ya ce, “sannan kuma sai wa?”
Sai Iblis ya ce, “sannan kuma sai
talaka mai yawan hakuri matukar
bai kai karar cutarsa ba.”
Sai Manzon Allah SAW ya ce, “yaya
aka yi ka san cewa shi mai hakuri ne?”
Sai Iblis ya ce, “ya Muhammadu, ai
idan ya kai kara a halin da yake ciki
ga wani mutum irinsa har kwana
uku to ba za a rubuta masa ladar
masu hakuri ba.” Sai Manzon Allah SAW yace, “sannan
kuma sai wa?”
Sai Iblis ya ce, “sannan kuma
mawadaci mai yawan godiya.”
Sai Manzon Allah SAW ya ce, “yaya
aka yi ka san cewa shi mawadacin mai yawan godiya ne?”
Sai Iblis ya ce, “idan na ga
mawadaci yana riko da halali kuma
yana ajiye shi a inda ya dace.”
Sai Manzon Allah SAW ya ci gaba da
tambayar shaidan, “To yaya kake samun kanka idan al’ummata suka
tashi zuwa Sallah?”
Sai shaidan ya ce: “ya Muhammadu
idan al’ummarka suka tashi zuwa
Sallah, sai zazzabi ya kama ni da
masassara.” Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to
idan suka dauki azumi fa?”
Sai Iblis ya ce, “sai a daddaure ni
har sanda suka sauke azuminsu.”
Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to
idan kuma suna aikin Hajji fa?” Sai Iblis ya ce, “idan suna aikin hajji
sai a haukatar da ni.”
Sai Manzon Allah SAW ya ce, “idan
suna karatun Alkur’ani fa?”
Sai Iblis ya ce, “sai a narkar da ni,
kamar yadda ake narkar da darma a cikin wuta.”
Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to
idan suka yi sadaka fa?”
Sai Iblis ya ce, “sai in ji kamar mai
sadakar nan ya dauki zarto ya raba
ni gida biyu.” Sai Manzon Allah SAW ya ce, “me ya
kawo haka, ya aba marrata?”
Sai Iblis ya ce, “domin a cikin
sadaka akwai kyawawan abubuwa
guda hudu:
1. Hakika mai sadaka Allah Madaukaki Yana saukar masa da
albarka a cikin dukiyarsa.
2. Kuma Yana soyar da shi a wajen
bayinSa.
3. Kuma Yana sanya sadakarsa ta
zama hijabi tsakaninsa da wuta. 4. Kuma Ubangiji Yana yaye masa
talauci da masifu.”
Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to me
kake cewa a kan Abubakar?”
Sai Iblis ya ce, “ya Muhammadu, ai
Abubakar bai bi ni ba a lokacin Jahiliyya. Yaya zai bi ni a wannan
zamani?”
Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to me
kake cewa a kan Umar?”
Sai Iblis ya ce, “ai ban taba cin karo
da Umar ba face sai na yi ta kaina.” Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to me
kake cewa a kan Usman?”
Sai Iblis ya ce, “ina jin kunyar
wanda mala’ikun Ubangiji suke jin
kunyarsa.”
Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to me kake cewa a kan Aliyu?”
Sai Iblis ya ce, “kaicona, ina ma na
rabu da shi , shi kuma ya rabu da ni.
Amma ina! bai yarda da haka ba.
Sai Manzon Allah SAW ya ce, “na
gode wa Allah da Ya azurta al’ummata, kai kuma Ya tsiyataka,
har zuwa ranar Alkiyama.”

No comments:

Post a Comment