Muna Murna Da Ziyarar Da Aka Kawo Mana

Muna Godiya Da Farin Ciki Ga Duk Gudun Mawar Shawara Dag Zaku Iya Bamu,

Sai Munji Daga Gare ku.

Saturday, June 25, 2011

MAKIRCIN SHAIDAN GA DANADAM (2)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai
jinkai. Dukkan yabo da godiya na
Allah ne, Ubangijin halittu. Tsira da
amincin Allah su tabbata ga
mafificin halittu, Muhammadu dan
Abdullahi, sallallahu alaihi wasallam, tare da alayensa da
sahabbansa da duk wanda ya bi
tafarkinsu har zuwa ranar karshe.
Bayan haka, yau ga ci gaban
tattaunawar Manzon Allah,
sallallaahu alaihi wasallam da shaidan. Mun kwana daidai inda
Ma’aiki, sallallaahu alaihi wasallam, ya yi godiya ga Allah da Ya azurta
al’ummarsa kuma ya tsiyata shaidan. Daga nan:
Sai Iblis ya ce, “ba mai yiyuwa ba ne. Ina ka ga tsirar al’ummarka alhali ni ina raye zuwa lokaci abin
sani? Yaya za ka dinga farin ciki a
kan al’ummarka, alhali ni ina mai shiga cikin jikinsu da magudanar
jininsu da tsoka, kuma alhali su ba
sa ganina. Kai, wallahi na rantse da
Wanda Ya halicce ni kuma Ya
jinkirta min zuwa ranar tashi, sai na
hallakar da su gabaki dayan su. Jahilansu da malamansu. Wadanda
suka iya karatu da wadanda ba su
iya karatu ba. Da kuma masu bautar
Ubangiji, sai dai bayin Ubangiji
tsarkakakku. ” Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to su wane ne tsarkakakku a wajen ka ?” Sai shaidan ya ce, “ya Muhammadu, yanzu ba ka san cewa duk wanda
yake kaunar duniya da dukiya ba ya
cikin tsarkakakkun bayin Allah
Madaukaki ba? Amma idan ka ga
mutum ba ya kaunar duniya, ba ya
kaunar dukiya kuma ba ya kaunar yabo balle a yabe shi, to hakika na
san wannan yana daga cikin bayin
Allah tsarkakakku. To wannan sai na
rabu da shi domin ya fi karfina.
Hakika idan bawa ya dawwama a
kan son dukiya da son a yabe shi kuma zuciyarsa ta ta’allaka sha’awe-sha’awen duniya, to hakika shi wannan ya tattare dukkan abin
da na siffanta maku.
“ Yanzu ya Muhammadu, ba ka san son dukiya na daga cikin manya-
manyan zunubai ba? Yanzu ya
Muhammadu, ba ka san cewa son
shugabanci yana daga cikin manya-
manyan zunubai ba? Ya
Muhammadu, ba ka san cewa ni ina da ’ya’ya dubu saba’in ba? Kuma kowane daya daga cikinsu yana da
rundunar shaidanu guda dubu
saba’in a karkashinsa? Akwai daga cikinsu wanda na
wakilta shi a kan tsofaffi, amma
matasa kuwa babu wani sabani
tsakanina da su. Amma kananan
yara kuwa sai shaidanu su dinga
wasa da su kamar yadda suka ga dama. Akwai daga cikinsu wanda
hakika na wakilta shi ga masu
bautar Ubangiji. Akwai daga cikinsu
wanda na wakilta shi ga masu
gudun duniya, suna kaiwa suna
komowa a tsakaninsu, kuma suna fitar da su daga wannan hali zuwa
wancan hali, daga wannan kofar
zuwa waccan kofar, har sai sun fitar
da su daga hanyoyi zuwa wadansu
hanyoyi. Ni kuma sai na bata musu
tsarkin aikinsu, alhali suna masu bautar Allah Madaukaki ba tare da
tsarkakewar aiki ba, alhali kuma su
ba su sani ba.
“ Yanzu ya Muhammadu, ba ka da labarin Barsisi mai ibada cikin
addinin Nasara, wanda ya shafe
shekara saba’in [70] yana tsarkake aikinsa saboda Ubangiji Madaukaki,
har sai da ta kai Allah Ya warkar da
marasa lafiya da addu’arsa, amma ban bar shi ya kai ba. Sai da na sa
shi ya yi zina kuma ya yi kisan kai,
kuma ya zama kafiri. Ai shi ne
wanda Ubangiji Ya ambace shi a
cikin Littafinsa Mabuwayi da fadinSa
cewa: ‘Cewar misalin shaidan ne a yayin da ya ce da dan Adam
kafirce’. A lokacin da ya kafirce, sai shaidan ya ce da shi. ‘To ni babu ni, babu kai, domin ni ina tsoron Allah,
Ubangijin halittu”. “Yanzu ya Muhammadu, ba ka san cewa dukkan karya daga gare ni
take ba? Kuma ni ne wanda ya fara
yin karya? Kuma ni ba ni da aboki
sai makaryaci, wanda ya yi
rantsuwar karya, to shi ne
masoyina. “ Ya Muhammadu, yanzu ba ka san ni ne wanda ya rantse wa Hauwa’u da Adamu da Allah a kan cewa ni
mai nasiha ne a gare su ba ? Kuma
rantsuwar karya ita ce take faranta
min zuciya. Giba da annamimanci
kuwa su ne kayan marmarina da
farin cikina. Shaidar karya kuwa ita ce sanyin idanuwana, kuma ita ce
abar yardata. Wanda ya yi
rantsuwar shirka kuwa to ya
kusanta, ya zama babban mai
zunubi ko da rantsuwar shirkar nan
sau daya ne kawai, kuma ko da gaskiya ya fada, domin kuwa
wanda ya saba wa harshensa da
rantsuwar shirka, to hakika an
haramta masa matarsa. Sannan
kuma ba za su gushe ba suna
mazinata, kuma suna hayyafa har zuwa ranar Alkiyama, sai sun
kasance ’ya’yan zina gabaki dayansu. Sai a shigar da su wuta
saboda kalma kwaya daya tak.
“ Ya Muhammadu, hakika daga cikin al’ummarka akwai wanda yake jinkirta sallah daga lokacinta zuwa
wani lokacin. A duk yayin da yake
so ya mike zuwa sallah sai na tsare
shi ina yi masa waswasi, kuma sai
na ce da shi ‘akwai sauran lokaci, ba ka karasa abin da yake gabanka ba ’, har dai ya jinkirta sallah ya yi ta ba
a kan lokacinta ba. Sai a nannade
masa sallarsa a maka masa ita a
fuskarsa. Idan na ga zai rinjaye ni,
ya yi ta a kan lokacinta, sai na aiko
masa da wani daga cikin shaidanun mutane, sai ya shagaltar da shi har
lokacinta ya wuce. Idan kuma ya
rijaye ni a kan wannan, sai na kyale
shi har sai ya fara yin sallar, sai na
dinga cewa da shi ‘dubi hagu, dubi dama’, to idan na ga haka, sai raina ya yi mini dadi, sai na shafi fuskarsa
kuma na tsotsi tsakanin idanunsa
sai na dinga cewa yanzu ka aikata
abin da har abada sallarka ba za ta
gyaru ba’. “Kuma ka sani, ya Muhammadu, wanda ya yi waiwaye a cikin
sallarsa, to Ubangiji zai sa a mako
masa sallarsa a fuska. Idan kuwa ya
rinjaye ni a cikin sallarsa ya zo ya yi
ta shi kadai, to sai na sa shi ya yi ta
a cikin gaggawa sai ya dinga dungura ta kamar yadda zakara
yake tsattsagar dawa, nan da nan
kamar koton kurciya. Idan kuwa ya
rinjaye ni har na ga zai yi sallah a
cikin jama’a, to ba kyale shi zan yi ba. Sai na daura masa linzami. Ina
mai daga kansa kafin liman ya
daga. Kuma ina mai sunkuyar da
kansa kafin liman ya sunkuya. Kai
kuma ka sani, ya Muhammadu, duk
wanda ya aikata haka to ba shi da sallah. Idan kuma ya rinjaye ni a
nan, to sai na umarce shi ya dinga
tantankwasa hannunsa alhali yana
cikin sallar. Wanda ya aikata haka
kuwa, ni yake yi wa tasbihi a cikin
sallarsa. Idan kuwa ya rinjaye ni a nan, to sai na yi masa busa a cikin
hancinsa, wacce take za ta sa shi ya
yi hamma a cikin sallarsa, idan bai
toshe bakinsa a yayin da yake
hammar ba, to sai in shiga cikin
bakinsa. To wannan sai ya kara masa son duniya da kaunarta. Sai
ya kasance ba ya sauraren kowa sai
ni, kuma ba ya biyayya ga kowa sai
ni.
“ Ya Muhammadu, ina aikin al’ummar taka yake? Ga ni ina umarnin talakawa, ina ce musu
sallah ba ta talakawa ba ce, ta
wadanda Allah Ya yi wa ni’ima ce. Kuma ina cewa da marar lafiya,
sallah ba wajibi ba ce a kan marasa
lafiya, sallah ta wadanda Allah Ya yi
wa ni’ima da lafiya ce. Ba ku ji Ubangiji Madaukaki yana cewa:
“Babu laifi ga marar lafiya” , idan kuwa sallah ta kubuce ma marar
lafiya har ya mutu, to hakika ya
mutu kafiri, idan kuwa ya mutu
yana tarikus-salat a yayin rashin
lafiyarsa to hakika zai sadu da
Ubangiji Yana mai fushi da shi. “ Ya Muhammadu, idan abubuwan da nake gaya maka karya ne, to roki
Ubangiji Ya maida ni toka. Ya
Muhammadu, yaya za ka yi farin ciki
a kan al’ummarka, alhali na kasance ina fitar da sudusin al’ummarka daga Musulunci?” Sai Manzon Allah SAW ya ce, “ya kai la’antaccen Allah, wane ne abokin zaman ka?” Sai shaidan ya ce: “maciyin riba shi ne abokin zamana.” Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to wane ne abokinka?” Sai shaidan ya ce “barawo shi ne abokina.” Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to wane ne masoyinka?” Sai shaidan ya ce, “Tarikus-Salat (wato mai barin sallah) shi ne
masoyina.” Sai Manzon Allah SAW ya ce, “ya la’antaccen Allah, to mene ne yake karya doron bayanka?” Sai shaidan ya ce, “kururuwar doki a wajen daukaka kalmar Allah. ” Sai Manzon Allah SAW ya ce, “to mene ne yake narkar da jininka ?” Sai shaidan ya ce, “tuban mai tuba, shi ne yake narkar da ni.”

No comments:

Post a Comment